Yayin da ya rage kwanaki 10 a yi babban zaben kasa, Fasto Elijah Ayodele yayi gargadin cewa rikici zai iya barkewa bayan zaben.
Elijah ya bayyana cewa rikici ka iya barkewa idan dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Ahmad Tinubu da dan takarar shugaban kasa na Labour party, Peter Obi suka fadi zabe.
Saidai Ayodele yace babu wani juyin mulkin da zai faru a Najeriya.
Daily Post ta ruwaitoshi yana cewa, Hukumar zabe me zaman kanta, INEC ce zata tantance makomar kasarnan.
Yace ida ta yi abinda ya kamata, za’a ga nasara, idan kuma ta aikata ba daidai ba, to lallai akwai matsala.