Monday, March 30
Shadow

Ighalo ya samu sabuwar garabasar samun euros 400,000 a kowane mako na tsawon shekaru biyu

An samu labari daga Sky Sport cewa Shanghai suna so dan wasan nasu ya dawo Asiya in an gama buga kakar wasan premier lig. Kuma sun ce in ighalo ya dawo Shanghai ya fasa zama a United zasu ringa biyan shi euros in 400,000 a kowane mako har na tsawon shekaru biyu.

 

Ighalo ya aminta da ragin albashi don ya cika burin shi na buga wasa a kulob din da yake so tun yarinta shi. Kuma yayi matukar mamaki ganin cewa ya ci kwallaye har guda hudu a wasanni guda takwas daya buga a kulob din United.

 

An daga wasannin premier lig saboda an kulle kasar UK don ganin cewa an dakile yaduwar cutar coronavirus/Covid-19.

 

FA ta sanar cewa ba za’a dawo wasa ba har sai ranar alhamis 30 ga wata afrilu.

 

Ya kamata United ta yi gaggawar aikata wani abu in har tana so ighalo yayi burus da sabuwar garabasar da ya samu a China.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwx

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *