Wani malamin addinin musulunci a kasar Kenya ya buƙaci kotu da kada ta sake shi daga gidan yari duk da cewa an wanke shi daga laifukan ta’addanci.
Guyo Gorsa Buru ya ce yana fargabarza a iya sace shi ko kashe shi da zarar an sako shi kamar yadda ake zargin ya faru da wasu da ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci.
An kama shi ne a 2018 kuma an tuhume shi da mallakarabubuwan da ke nuna yana da alaƙa da ƴan ta’adda da kuma haɗa kai da mayakan al-Shabab na Somaliya.
Kotun da ke babban birnin ƙasar ta ba shi damar ci gaba da zama a gidan yarin na tsawon kwana 30.
Lauyansa ya roƙi kotun ta ba shi tabbaci na kariya idan har an sake shi.