Wasu ma’aurata dake da ‘ya’ya 5 suka kuma rungumi tsarin hana haihuwa saboda a tunaninsu yaran sun ishesu, a yanzu matar ta haifi ‘yan hudu a lokaci guda.
Christopher Agbo da mataraa auna zaunene a Sabon Tasha dake Gwagwa a babban birnin tarayya, Abuja.
Kuma matar tasa ta haihune a Asibitin Kubwa ranar Alhamis. Mijin yace sun yi amfani da tsarin hana haihuwa da ‘ya’ya 5 da suke dasu sun ishesu amma ruk da haka sai ga matarsa ta sake haihuwa.
Da aka tambayi likitan yace basu yi amfani da tsarin hana haihuwar ne da kyau ba shiyasa matar ta haihu.