fbpx
Saturday, August 20
Shadow

ILIMIN RAYUWA BA DOLE SAI A AJI BA: Karanta kuji wani babban Darasi

ILIMIN RAYUWA BA DOLE SAI A AJI BA.

Wani Dattijo ya kira yaronsa a yayinda yake fama da jinyar da ya yanke tsammanin cigaba da rayuwa. Dattijon yace da yaron sa, ‘Duk sanda na mutu kaje wurin abu shida su koya maka rayuwa.” Yaron yace “su waye wa’yannan Baba?” Dattijon yace “Kare, Maciji, Kulɓa, Tsohon doki, Kiyashi da Balbela.”

Bayan mutuwar Dattijon yaron ya fara zuwa wurin Kare. Kare yace “Yaro zo in koya ma rayuwa.” Yaron kuwa ya bi bayan kare har suka je inda taron wasu almajirai yake. Almajiran na ganin kare sai suka fara yekuwa, Kare! Kare!! Kare!!! Kafin kace kobo sun kora shi da jifa.
Yaron ya cigaba da bin kare har zuwa inda mafarauta suke. Mafarautan na ganin kare sai suka tare shi hannu bibbiyu, suka bashi abinci da ruwa. Kare ya juya ya kalli yaron nan. Yace yaro kaga abinda ya faru ko? Yace Eh, na gani. Kare yace daga yau ka ringa bin wanda ke son ka.
Daga nan yaro ya wuce wurin Kulɓa. Kulɓa ta ja yaro suka tafi har inda wasu magina suke. Sai ta yi zurrr! ta shige cikin wani saƙo. Maginan nan suke ce Maciji! Maciji!! Maciji!!! Sai kowa ya nemi mabugi. Wani diga, wani cebur, wani gatarin sassaƙar bulo. Suna gama tone wannan saƙo sai suka ga kulɓa, sai suka ce “Mtsww! Ashe ma kulɓa ce.” Kowa ya fita harkar ta suka cigaba da aikin su.

Kulɓa ta kalli yaro tace, “A koda wane lokaci ka yi ƙoƙarin suffanta da mutanen kirki. Wannan sai ya nisantar da kai daga sharrin mutane. Kaga bana cutarwa, amma kama da na ke yi da maciji ya jefa rayuwa ta cikin baraza.”

Yaro ya wuce zuwa ga Balbela. Tace yaro zo muje. Yaro ya bita har zuwa inda wasu shanu ke kiwo. Sai ta ringa bin bayan su a hankali. In sun take fara ko ƙwari sai ta cinye. A haka har ta ƙoshi. Tace yaro kaga abinda ya faru ko? Yace eh na gani. Tace to kada ka yi ƙoƙarin shiga gaban manya, in ba haka ba zasu take ka, su lahanta ka. Amma in ka bi su a baya sau-da-ƙafa sai ka moru da su.

Karanta wannan  Yadda yarinya 'yar shekara biyu ta kashe maciji bayan ya sareta

Daganan yaro ya wuce zuwa ga Maciji. Maciji yace “yaro ka zo ɗaukar darasi?” Yaro yace “eh.” Maciji yace kagan ni nan duk cikin dabbobi ba wanda ya kaini kyawun halitta, amma baki na ya ja min kowa yana guduna. Duk sanda a ka ganni hankali ba zai kwanta ba sai an kashe ni. To ka kiyaye bakin ka, sai jama’a su so ka. Su kuma samu natsuwa da kai a cikin zantukan su.

Daga nan yaro ya wuce zuwa ga kiyashi. Kiyashi ya ja shi suka tafi har suka cimma wani mushen fara. Sai kiyashi ya koma ya gayyato danginsa suka ja wannan mushen fara har muhallinsu. Kiyashi yace da Yaro. Komi za ka yi ka ringa neman shawara ga danginka (mutane), aikin ka ba zai ɓaci ba, kuma zumuncin ku zai ƙara ƙulluwa.

Daga ƙarshe yaro yaje wurin tsohon doki. Tsohon doki yace, ka ganni nan, lokacin da ina da ƙuruciya ta sarki ne ke hawa gadon baya na. Kullum cikin kula a ke da ni. Amma yanzu abinci ma sai na yi kuka sannan a bani. To ina gargaɗarka da ka yi amfani da ƙuruciyar ka don moriyar tsufan ka. Lokacinda kake samu ka yi ma tsufanka tanaji.
Allah yasa mu iya
By dutsen ma

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.