fbpx
Monday, August 15
Shadow

Ina alfahari APC tayi amfani da tsarina ta mika ragamar NNPC hannun ‘yan kasuwa bayan tace min mara kishin kasa a lokacin dana ce zan yi hakan, cewar Atiku Abubakar

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yayi tsokaci kan miga ragamar NNPC hannun ‘yan kasuwa da shugaba Buhari yayi.

Inda yace a shekarar 2018 shine yace zai mika ragamar kamfanin hannun ‘yan kasuwa don a habaka shi idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Amma jam’iyyar APC ta soke shi cewa zai sayar da kasa ne kawai idan aka zabe shi, kuma yanzu ita gashi ta mika ragamar kamfanin hannun ‘yan kasuwar.

Amma duk da haka ya jinjina masu yace yana alfahari da suka yi amfani da tsarin shi, sai dai fa duk da haka akwai gyara sai ya hau mulki sannan ya cigaba da habaka kamfanin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.