Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana alfahari da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
Ya bayyana hakane a cikin sakon taya gwamnan murnar cika shekaru 45 da yayi a yau, Alhamis, 18 ga watan Yuni.
A sakon da shugaba Buhari ya fitar ta hannun me magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya bayyana gwamna Yahaya Bello a matsayin dan Jam’iyyar APC me matukar biyayya.
Shugaba Buhari yace yana taya gwamnan murna yanda ya samu dama cikin shekarun kuruciya yana bautawa jama’aishi.