Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, yana alfahari da barin tarihin yaki da rashawa me kyau a Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa, zai ci gaba da fafutukar yaki da rashawa da cin hanci bayan ya bar kujerar mulkinsa.
Shugaban kasar ya bayyana hakane a matsayin sakonsa na ranar yaki da rashawa ta Africa a matsayinsa na shugaban kungiyar yaki da rashawa ta nahiyar.
Kakakin shugaban kasar, Femi Adesina ne ya bayyana haka a sanarwar bayan jawabin da shugaban kasar yayi.