Shugaban kasar Najeriya, Mejo Janar Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana alfahari daya kasance a mulkinsa ne aka samu cigaban harkar man fetur wanda zai samar da tsaro kuma ya habaka tattalin arzikin Najeriya.
Shugaban ya bayyana hakan ne bayan ya kaddamar da sabon tsarin kasuwanci a kamfanin NNPC Limited a babban birnin tarayya Abuja yau.
Inda yace wannan sabon tsarin na kasuwanci zai kawo cigaba sosai a kasa kuma harkar mai zata kara daukaka sannan kasar Najeriya zata tsaro sosai.