fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Ina Allah wadai da kashe mutanen da aka yi a Kaduna>>Shugaba Buhari

Shugaba Buhari yayi Allah wadai da kisan mutane da aka yi a kauyen Kauran Fawa dake karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

 

Shugaban ya bayyana cewa, yana Allah wadai da kisan kuma abin bai masa dadi ba.

 

Akalla mutane 38 ne harin ya hallaka kamar yanda Rahotanni suka nunar.

 

A sakon da kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya fitar ya bayyana cewa, Wannan harin ba wanda za’a amince dashi bane.

 

Shugaban ya kuma yi Allah wadai da hare-haren da aka kai kananan hukumomin Chukun, Birnin Gwari, Zangon Kataf da Igabi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.