Uban kasa a jihar Kaduna, Dr. Hakeem Baba Ahmad ya baiwa gwamnan Kadunan shawarar cewa kada ya tsawaita maganar nadin sabon sarkin Zazzau.
Yace dalili kuwa shine Allah ne kawai me yin daidai kuma ba za’a iya farantawa kowa ba. Yace tsawaita nadin sarkin ka iya sa kutane su fara zargin Gwamnan da cewa, yana son nada nasa sarkin ne.
With due deference for the need to be thorough, it is important to remind Gov el-Rufai that only God’s choice is perfect.The longer the process is delayed, the more widespread the speculations that govt is looking for its own Emir, not the Emir of Zazzau.There is history here too
— Dr. Hakeem Baba-Ahmed. (@baba_hakeem) September 25, 2020
Dr. Hakeem ya bayar da wannan shawara ne ta shafinsa na Twitter.
A jiyane dai gwamnan ya tabbatar da karbar sunayen mutane 11 wanda daga cikine za’a dauki wanda za’a nada Sarki.