fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

“Ina baku hakuri akan karancin man fetur da rashin wutar lantarki”>> Buhari ya fadawa yan Najeriya daga Landan

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana bacin ransa akan mawuyacin halin da Najeriya ke ciki na rashin man fetur da kuma wutar lantarki.

Inda yasha alwashin cewa nan bada dadewa ba komai zai daidaita domin gwamnati na iya bakin kokarinta akan lamarin.

Kuma shugaban kasar ya bayar da hakuri akan lalataccen man fetur din da aka shigo dashi kasar wan ya hallaka injina da kuma ababen hawa.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne daga Landan inda yayi tafiyar domin duba lafiyarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.