Tauraron mawakin Hausa, Nazir Ahmad Sarkin Waka ya bayyana cewa, shi yana da halin da ‘ya’yansa zasu yi karatu a gabansa shiyasa bai kaisu Almajirci ba.
Ya bayyana hakane a matsayin martani ga wani da ya tambayeshi mai yasa bai kai danshi Almajirci ba?
Nazir dai ya mayar da martani kan maganar da Nafisa Abdullahi ta yi kan haihuwar yara ana turasu Almajirci.
Nazir a wani sabon sako da ya saka yace, bai kamata ake Almajirci ba amma daga an shiga matsala sai ace a nemo su Alaramma koh?
Wato bai kamata aje almajiciba ko?amma ai ya kamata daga mun shiga matsala muce a nemo almajirai suyi sauka…😊Wai bana sonka amma ina son abun hannunka pic.twitter.com/uimKdPu3Zo
— Sarkinwaka (@real_sarkinwaka) April 24, 2022
Wato bai kamata aje almajiciba ko?amma ai ya kamata daga mun shiga matsala muce a nemo almajirai suyi sauka…😊Wai bana sonka amma ina son abun hannunka.