Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, yana da tabbacin tsare-tsarensa zasu sa ‘yan Najeriya su sake zabar APC a shekarar 2023.
Ya bayyana hakane a fadarsa yayin da ya karbi bakuncin shugaban APC, Sanata Abdullahi Adamu.
Kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu yace shugaba Buhari yace idan ya kalli irin ayyukan da yawa mata da matasa da kuma ci gaban da ya kawo ta fannin fasaha, kirkire-kirkire, Noma, da raya kasa duk zai ga cewa ‘yan Najeriya zasu zabi APC.