fbpx
Saturday, September 19
Shadow

Ina goyon bayan Obasanjo cewa Shugaba Buhari na raba kawunan ‘yan Najeriya>>Wole Soyinka

Babban Marubucin Najeriya, Wole Soyinka ya bayyana cewa yana goyon bayan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da cewa Najeriya bata taba samun rarrabuwar kai kamar a zamanin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba.

 

Soyinka ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar a yau inda yace duk da baya tare da Obasanjo amma maganar da yayi gaskiyace.

 

Yace a baya ya taba fadar cewa kada a kalli wanda yayi magana amma a kalli muhimmancin maganar da yayi. Maganar Gaskiya shine shugaba Buhari a mulkinsa yana can yana bacci amma na nan ana kashe mutane.

 

Soyinka yace a lokacin shugaba Buhari ne aka yi shugaban ‘yansanda wanda aka tura wajan aiki amma yaki zuwa kuma babu abinda ya faru. Yace tabbas Najeriya na gab da rabewa gaba daya a karkashin mulkin shugaba Buhari.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *