Fadar shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta bayyana cewa, shugaban kasan na goyon bayan Buhari dari bisa dari.
Kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka inda yace idan lokacin zabe yayi, ana yada maganganu kala-kala.
Yace ‘yan Jarida na yin dukkan kokarinsu wajan ganin sun fassara hotuna da maganganu da aka yi dan samun labarin yadawa.
Yace kuma abin sha’awa shine yanda aka kammala zaben fidda gwani na APC babu wanda yace bai yadda da zaben ba kima babu wanda yayi barazanar ficewa daga jam’iyyar.
Ya kara da cewa shugaba Buhari baya katsalandan a harkar zabe ko siyasa.
Yace shugaba Buhari ya bari an yi zaben gaskiya kuma hakan ya karawa ‘yan Najarian mutunci a Idon Duniya.