fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Ina haɗa aure sama da 300 a shekara>>Mai dalilin aure

Ina haɗa aure sama da 300 a shekara — Mai dalilin aure.

Hajiya Aisha Ahmed, mai sana’ar haɗa aure a Jihar Kano, ta ce ta na haɗa aure har sama da dari uku a shekara.

Ahmed, wacce a ke kira da Mai dalilin aure, ta kuma ce har tsakanin nakasassu ta ke haɗa auratayya.

Da ta ke bayani a wani shiri mai taken Barka da Hantsi a Freedom Radio, wanda Daily Nigerian Hausa ta saurara a yau Laraba, Mai dalilin aure ta ce ana samun wani lokacin matsaloli da har za ta kai ga an fasa aure.

A cewar ta, yawancin matan da ke tuntuɓar ta domin ta nemo musu mazajen aure, sai su ce dole sai mai kuɗi, inda ta ce hakan matsala ce da ke daƙile yin auren a wasu lokuta.

Ta ƙara da cewa suma mazan wani lokacin sai su ce sai mace mai kyau, fara mai gashi, inda ta ce wannan ma ya kan kawo cikas wajen yin auren.

Karanta wannan  Yadda abokai uku suka nutse a ruwa a Ƙaraye a Kano

Sannan ta baiyana cewa ta na yin bincike sosai, musamman ɓangaren addini, tarbiyya da sana’a kafin ta haɗa aure.

Sai dai kuma ta ce “mutane da yawa, daga duka ɓangaren mata da mazan, suna yawan kira na su ce in haɗa musu aure. Har da ma masu buƙata ta musamman.

” Duk mai bukata, zai yi mini waya. Daga nan kuma sai na tura musu hotuna ta WhatsApp su zaɓa. Duk wanda ko wacce ta yi, sai a haɗa auren. Kuma alhamdulillah, a na samun nasara domin a shekara ɗaya na kan haɗa aure sama da dari uku,” in ji ta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.