fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Ina jiwa Buhari tsoron idan ya sauka daga Mulki ya ji abinda ya faru a mulkinsa kar ya hadiyi zuciya>>Buba Galadima

Tsohon na hannun damar shugaban kasa, Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa yana jiwa shugaban kasar tsoron Bugun zuciya idan ya sauka daga Mulki ya ji abinda ya faru a mulkin nasa.

 

Ya bayyana hakane a lokacin da yake amsa tambaya daga Sunnews akan binciken da majalisa jewa wasu masu mukamai a mulkin shugaban kasar.

Yace duk wadannan abubuwa dake faruwa dama can su sun fadesu saidai a lokacin an rika sukarsu, maimakon a kalli sakon da suke kokarin isarwa sai aka rika kallonsu cewa basu kai su fada a ji ba.

 

Yace yawancin mutanen da suka samu mukamai a mulkin shugaban kasar makudan kudade suka bayar aka basu wadannan mukamai.

Karanta wannan  Duk shekara, gwamnati na ware biliyan 1 dan tallafawa 'yan Najariya>>Minista Sadiya

 

Yace to dole fa idan suka samu mukaman su yi kokarin ganin sun mayar da kudin da suka kashe wajan samunshi. Yace ta yaya mutane irinsu Godswill Akpabio zasu yi wani abin arziki?

 

Yace yawancinsu mutanene dake da laifi suna neman hanyar da zasu tsira shine suke zuwa a basu mukami amma shugaban ya kasa ganin haka. Yace yanawa shugaban fatan Alheri amma yana fargabar kada bayan ya sauka daga mulki ya ji abinda ya faru a gwamnatinsa ya hadiyi zuciya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.