Babbar likitan yara Dr. Rasheedat Ibrahim dake jihar Ilorin tayi kira ga iyayen yara cewa su daina baiwa ‘ya’yansu ‘yan kasa da shekaru biyar maganin syrup na mura.
Inda tace maimakon magance murar maganin ka iya jawo wata cutar ta daban ga lafiyar yara masu karancin shekaru.
Likitar ta kara da cewa yara masu shekaru kasa da biyar basa iya yin kaki koma yazo sai dai su hadiye abunsu, kuma babu likitan da zaice a kawo kakin yaro ayi gwaji wata cuta.
Saboda haka tana kira ga iyayen yara su kula su daina basu maganin surup na mura don inganta lafiyarsu.