Sanata Dino Malaye ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta kwantar da hankalinta kawai don ta lashe zaben shekarar 2023 kawai sai dai shirye shiryen karbar mulkin.
Inda yace shi yana mai baiwa Atiku Abubakar shawara kawai yaje ya fara shirye shiryen karbar mulkin Najeriya domin shine shugabanta nan bada dadewa ba.
Dino yace Atiku ya kerewa Tinubu ta fannin siyasa kuma shine ya janyewa MKA Abiola, sannan ya taba yin mataimakin shugaban kasa.
Saboda haka yanada ilimin siyasa sosai da zai mulka Najeriya fiye da Bola Ahmad Tinubu.