fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Ina sane da halin matsin da kuke ciki, amma ku sani ba da gangan muka dauki matakai masu tsauri ba>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya bukaci Musulmai su kasance cikin cikin karfin gwiwa duk da halin da Annobar cutar Coronavirus/COVID-19 ta zo dashi.

 

Shugaban nya bayyana hakane a cikin sakon barka da Sallah da ya aikewa ‘yan Najeriya ta hannun me magana da yawunsa,Garba Shehu, kamar yanda ya bayyan a yau, Asabar.

Shugaban yace ba abune me sauki ba yin azumi ba tare da Sallar Taraweeh ba da kuma Tafsir ba yace amma hakan ya zama dole saboda dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.

 

Yace yana kira ga masu hali daga ciki su ci gaba da taimakawa wanda basu da shi dan a samu a gudu tare a tsira tare.

 

Yace yana yabawa da sadaukarwar da musulmai da Kiristoci suka yi na hakura da taron ibada saboda wannan cuta.

Karanta wannan  Don Allah ka dauki mace a matsayin abokiyar takararka, matan APC suka roki Tinubu

 

Yace yana sane da hali  matsin da Mutane ke ciki bisa wannan matakai da aka dauka. Musamman masu kasuwanci da suka hakura da kasuwancinsu.

 

Yace babu gwamnatin da dagangan zata dauki irin wadannan matakai masu tsauri akan ‘yan kasar ta saidai idan ya zama dole.

 

A karshe shugaba Buhari ya yiwa ‘yan Najeriya fatan Allah ya kawo musu saukin halin matsin da suke ciki sannan kuma yace yana musu barka da Sallah.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.