fbpx
Saturday, November 28
Shadow

Ina So A Dawo Da Rundunar SARS Jihata>>Gwamna Zulum

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, a ranar Talata, 13 ga watan Oktoba, ya bukaci hukumar yan sanda da ta tura jami’an rundunar SARS da aka rushe zuwa jihar domin bayar da gudunmawa a yaki da yan ta’addan Boko Haram.

 

An dai soke sashin rundunar ta yan sanda sannan aka rarraba jami’ata zuwa wasu bangarorin biyo bayan zanga-zangar kawo karshen rundunar SARS da aka gudanar a kasar. Kasa da kwanaki biyu bayan soke rundunar yan sandan, an sake gudanar da gagarumin zanga-zanga kan ayyukanta a ranar Talata a fadin kasar.

Zulum ya yi kiran ne a lokacin da wata tawaga karkashin jagorancin ministan cikin gida, Rauf Argebesola suka gana da shi a gidan gwamnati, Maiduguri, Daily Trust ta ruwaito.

 

Zulum ya goyi bayan SARS, yana so a dawo da jami’an rundunar jiharsa.

 

Gwamnan ya ce jami’an rundunar da aka soke sun taka muhimmiyar rawar gani a ayyukan yaki da ta’addanci da karfinsu musamman a yaki da Boko Haram. Ya ce: “Ba ma goyon bayan cin zarafi daga kowani jami’in tsaro, amma maganar gaskiya, a nan jihar Borno bai kamata a wofantar da kokarin jami’an SARS ba a yaki da suke da ta’addanci. “Suna kokari matuka wajen magance matsalar tsaro a jihar Borno. Sun taimakawa kokarin rundunar sojin Najeriya sosai,” inji Zulum.

Rariya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay youLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *