Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya bayyana cewa yana yiwa mataimakin shugaba Buhari, Osinbajo fatan samun sauki kan tiyatar da aka yi masa.
A ranar asabar ne aka yiwa mataimakin shugaban kasar tiyata a kafarsa bayan ya samu karaya a wasan kwallon aquash.
An yiwa mataimakin shugaban kasar tiyata ne a Ikeja dake jihar Legas, kuma aikin yayi kyau an samu nasara.