Mataimakiyar dan takarar gwamnan jihar Legas na PDP, Funke Akindele ta bayyana dalilin dayasa zata kayar da APC a zabe mai zuwa.
Funke ta bayyana dalilin nata ne yayin da take ganawa da manema labarai na Channels, biyo bayan APC tace babu abinda zata tsinanawa PDP dashi a zaben gwamnan jihar.
Inda tace tanada mabiya sama da miliyan 20 a kafafem sada zumunta kuma ashirye suke dasu zabeta a zaben zuwa, sanna a jihar bakidaya tanada mabiya sosai.