Hukumar zabe me zaman kanta, INEC ta baiwa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki Shedar sake lashe zabe a karo na biyu.
An mikawa Obaseki takardar shaidar lashe zabenne tare da mataimakinsa, Philip Shu’aibu a yau, Talata.
Obaseki ya lashe zabenne bayan da ya doke abokin hamayyarsa, Fasto Ize-iyamu da tazarar kuri’u sama da dubu 80.