fbpx
Thursday, June 30
Shadow

INEC ta tsawaita lokacin zabukan fitar da gwani a Najeriya

Hukumar zaben mai zaman kanta a Najeriya INEC ta tsawaita lokutan zabe tare da kara lokacin zabukan fitar da gwani.

Hukumar INEC ta kara tsawaita lokacin ne bayan tattaunawa da shugabannin jam’iyyun siyasa 18 da aka yi wa rijista.

A yayin taron wanda aka yi a hedikwatar INEC a Abuja, kwamitin ba da shawarwari tsakanin jam’iyyu ya nemi a kara wa’adin mako guda ga jam’iyyun domin kammala zabukansu na fidda gwani.

Shugaban kwamitin Injiniya Yabagi Yusuf Sani ne ya nemi INEC ta dage ainihin lokacin da ta sanya na farko na ranar 3 ga watan Junin gobe.

Leave a Reply

Your email address will not be published.