An kona Ahmad Usman mai gadin wata kasuwa a Abuja saboda ya zagi fiyayyen halitta Annabi Muhammadu S.A.W bayan da ya samu sabani da wani malamin addini dan kasuwar, Malam Lawan.
Malan Lawan ya kasance mai sayar da doya a kasuwar kuma ya samu sabani da Usman ne saboda Usman ya umurce shi ya kulle shago kamar yadda dokar kasuwar ta tanadar na rufe shaguna karfe 12 na dare.
Amma Lawan yaki bin dokar har ta kaiga Usman yace masa zai kama shi kuma koda annabi zai zo ya roqe shi ba zai taba sakinsa ba, amma daga bisani sun sasanta junan su da misalin karfe daya na dare kowa ya tafi ya kwanta.
Abokin aikin Usman, Bakko ya bayyana cewa washe gari ranar sati Malam Lawan yazo da tawagarsa da misalin karfe 1 na rana sun zargi Usman da zagin Annabi sun zane shi kuma sun kona shi da taya har ya mutu.