fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Innalillahi wa inna Ilaihi raji’un: An kama matasa na saka Hijabi suna shiga cikin mata yayin sallar Taraweeh suna taba musu jiki a Kaduna

Wani abin takaici ya faru a jihar Kaduna yayin da ake tsaka da watan Azumin Ramadana da ake son musulmai su koma ga Allah dan neman Rahama da gafara.

 

Sallar Taraweeh na daya daga cikin muhimman ibadun da ake a watan na Ramadana wanda kuma mata da maza sukan halarta.

 

A yayin Sallar ne dai aka kama wasu matasa a wasu yankunan Kadunan na saka Hijabi su badda kama su shiga cikin mata masu sallar Taraweeh suna taba musu jiki.

 

Lamarin ya faru a unguwannin Tudun Nupawa da kuma wasu unguwanni dake cikin jihar ta Kaduna.

 

Hakanan an samu wasu matasan yayin da ake sallar suna buga ababen fashewa dake saka tsoro a zukatan mutane.

 

Daya daga cikin limaman yankin, Malam Habibu ya bayyana takai ci akan lamarin inda yayi Addu’ar Allah ya shiryar da irin wadannan matasa masu mugayen hali.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *