Shugaban hukumar ‘yan sanda Alkali Usman Baba yasha alwashin kawo karshen matsalar tsaro da kuma barayi a kasa Najeriya.
Hukumar ce ta wallafa hakan a shafinta na Twitter yau ranar juma’a 29 ga watan Yuli.
Kasar Najeriya na fama da matsalar tsaro kuma hatta babban birnin yarayya Abuja ‘yan bindiga basu kyale ba amma hukuma na iya bakin kokarinta don magance wannan matsalar.
Yayin da hukumar ke kokarin kama ‘yan bindiga da kuma barayi a fadin kasar nan.