Insfeto janar na hukumar ‘yan sanda, Alkali Usman Baba ya bayar da umurni a fara kama masu yin wasan barkwanci da wasan kwaikwayo da kakin hukumar ‘yan sanda a Najeriya.
Inda kuma ya kara da cewa sauran mutanen dake saka kakin wa’yanda ba hukuma ba suma za a kamasu a hukunta su.
Ya kara da cewa hatta masu sayarwa mutane kakin sunayin amfani dashi za a kamasu domin wannan zagi ne ga hukumar ‘yan sandan Najeriya.