fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Insfeton ‘yan sanda na jihar Imo ya hallaka ‘yan bindiga biyu da suka kai masa a gidansa

Insfeton hukumar ‘yan sanda a jihar Imo yayi nasarar hallaka ‘yan bindiga guda biyu bayan sun mamaye masa gidansa a jiya alhamis.

Mai magana da yawun hukumar Michael Abattam ne ya bayyana hakan, amma bai bayyan su insfeton daya yi wannan namijin kokarin ba.

Yace sun kai masa harin ne a gidansa dake Orogwe a Owerri inda suka afka suka balla masa kofa, amma jami’in ya bude masu wuta har ya kashe guda a cikin su.

Kafin daga bisani suka tsere kuma ya kira abokan aikinsa inda aka kara ganin wata gawar ta wani dan bindigar kuma sun dauke makamansu bayan sun ya hallaka su.

Leave a Reply

Your email address will not be published.