fbpx
Monday, August 15
Shadow

Inspecta janar na ‘yan sanda ya baiwa iyalan jami’an da suka mutu a yaki da ta’addanci naira miliyan tara

Inspecta janar na ‘yan sanda ya baiwa iyalan jami’an ‘yan sanda da suka mutu a yaki da ta’addanci guda 15 naira miliyan 9.1 a jihar Abambra.

Kwamishinan ‘yan sandar jihar CP Echeng Echeng ne ya mikawa iyalan ‘yan sanda kudin wanda yace na ishoran jami’an ne aka mika masu.

Kuma ya kara da cewa kudin sun fito ne daga hannun shugabansu wato inspecta janar Usman Baba.

Inda ya umurce su dasu cigaba da aiki tukuru wurin yaki da ta’addanci a jihar ta Anambra.

Leave a Reply

Your email address will not be published.