fbpx
Saturday, August 8
Shadow

Inyamurai sunce sune da mulki a 2023, saidai wani basarakensu yace bafa zasu rika zagin Buhari ba su kuma yi tsammanin ya basu mulki ba

Wani Basarake wanda tsohon sojan Biafra ne a Enugu, Egwe Spencer Ugwuoke ya bayyanawa kabilarsa ta Inyamurai cewa su manta da maganar samun shugabancin Najeriya a shekarar 2023.

 

Yace Inyamurai basu da hadin kai sannan ba alkibla inda yace ba ko kananan Kabilu sun fisu tsara lamuransu.

Yace samun shugaban kasa Inyamuri abu ne da za’a dauki lokaci ana nema amma ba a shekarar 2023 ba.

 

Saidai kungiyar kare muradun Inyamurai ta Ohanaeze ta bakin me magana da yawunta, Uche Achi-Ogbaga ta bayyana cewa zata iya samun shugaban kasa a shekarar 2023.

 

Tace ba dolene Inyamurai su kasance a jam’iyya daya ba amma kuma hakan ba wai yana nufin kansu ba a hade yake ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *