fbpx
Thursday, May 19
Shadow

IPOB ce ke kashe mutane a jihohin Inyamurai>>Inji tsohon Mataimakin Nnamdi Kanu

Tsohon Mataimakin shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB dake son kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu watau Uche Mefor ya bayyana cewa, Kungiyar IPOB ce ke kashe Inyamurai a jihohin Inyamurai.

 

Yace maganar gaskiya IPOB ce ke kashe mutane kuma tana bibiya tana kashe mutanen da bata shiri dasu.

 

Yace abin bakin ciki ne yanda kungiyar ke kashe Inyamurai wanda suma ke son kafa kasar Biafra.

 

Ya bayyana hakane a shafinsa na Facebook.

 

Kungiyar IPOB dai ta sha musanta cewa ba itace ke kashe mutane a jihohin Inyamurai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.