fbpx
Friday, June 9
Shadow

Irin abubuwan jin dadin rayuwa da ‘yan kasar Libya ke mora lokacin mulkin Muammar Ghaddafi

Mutanen kasar Libya ne da taimakon kasashen yamma, suka kashe shugaban kasar su Muammar Ghaddafi, tun bayan kashe shugaban nasu sai kasar ta fada cikin wani yanayi na tashin hankali da rikici, kusan za’a iya cewa babu tsayayyar gwamnati, mayakan kungiyar ISIS, masu tsatstsauran ra’ayin addinin Islama sun shiga kasar, kusan ta zama wani yanki da suke cin karensu babu babbaka.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Duk da yake cewa an dan samu daidaito ta bangaren rashin gwamnati amma kwanannan aka fara jin duriyar bautar da mutane bakaken fata a kasar ta Libya, abinda Duniya take tunanin ta wuce da matsalarshi shekaru aruru, banda bautar ma, akwai cin zarafi, muzgunawa da kisa irin na wulakanci da wasu rahotanni suke nuna akewa bakar fatar acan.

Dama wani lokacin idan baka godewa rahamar Allah ba to zaka godewa azabarshi.

Mutanen kasar Libya lokacin mulkin tsohon shugaban kasarsu da ‘yan tawaye suka kashe watau Muammar Ghaddafi na daya daga cikin masu jin dadi ko kuma ma ace mafiya jin dadi a duk nahiyar Afrika.

Ga wasu bayanan abubuwan more rayuwa da mutanen kasar Libya ke dasu a lokacin mulkin Muammar Ghaddafi kamar yanda yake a ireport na kafar watsa labarai ta CNN.

‘Yan kasar ta Libya basa biyan kudin wutar lantarki: kyauta suke shan wuta.

Babu kudin ruwa a bashin da bankunan kasar suke baiwa ‘yan kasa, saboda bankunan kasar duk mallakin gwamnatine.

Idan dan kasar Libya ya kammala karatun jami’a, bai samu aiki ba,to gwamnati zata rika biyanshi rabin albashin da ake biyan me takardar karatu irin nashi dake aiki, har sai ya samu aikin yi.

Idan dan kasar Libya yana son kama sana’ar noma to gwamnati zata bashi filin noma, da gida, kayan aiki, iri da kuma dabbobin da zai fara dasu duk kyauta.

Tsohon shugaban kasar Libya, Muammar Ghaddafi ya gina madatsar ruwa ta noman rani mafi girma a Duniya, a kokarin gano man fetur, kasar ta gano wani ruwa tinjim a wani yanki na kasar, wannan yasa shugaban kasar yayi amfani da wannan damar wajan gina madatsar ruwa wadda babu irinta ko ina a Duniya, an ajiye bututu masu kai ruwan manyan biranen kasar ta Libya.

Karanta wannan  Dalibai a kasar China na biyan Naira Dubu 43,000 a kowanne awa dan a koyar dasu yanda ake murmushi

‘Yancin kane dole a baka gidan kanka a kasar Libya.

Idan mutane sukayi aure a kasar ta Libya, gwamnati na basu kudi, dalar Amurka dubu Hamsin, kwatankwacin naira miliyan goma sha takwas dan su fara rayuwa cikin sauki.

Ana baiwa yan ‘yan kasar ta Libya wani kaso daga cikin kudin da aka sayar da danyen man fetur din kasa.

Idan mace ta haihu, ana bata kyautar kudi, dalar amurka dubu biyar, kwatankwacin naira miliyan daya da dubu dari takwas.

Idan dan kasar Libya zai sayi mota, gwamnati ke biya mai rabin kudin motar.

Kowace litar man fetur ana sayar da ita akan kwatankwacin naira hamsin a lokacin shugaba Ghaddafi.

Da kudi, kwatankwacin naira hamsin da hudu, dan kasar Libya zai sayi biredi guda arba’in.

Ilimi da kiwon lafiya kyautane, ga kowane dan kasar Libya, kasar Libya nada mafi kyawu da inkantaccen harkar lafiya fiye da kowace kasar larabawa dana Africa.

Idan dan kasar Libya na bukatar fita kasar waje dan neman lafiya ko kuma ilimi, to gwamnatice zata dauki nauyinshi kuma duk wata za’a rika bashi dalar Amurka dubu biyu da dari uku, kwatan kwacin naira dubu dari takwas.

Kasar Libya bata da bashin kowace kasar Duniya a kanta, haka kuma tana da rarar kudi da suka kai dalar Amurka biliyan dari da hamsin, duk da yake cewa yanzu an sakawa kudin takunkumi.

Mutane da yawa sun fahimci cewa gamayyar kungiyar tsaro ta turawan yamma sun jagoranci kifar da gwamnatin Muammar Ghaddafine saboda (su saci) man fetur da kuma wasu sauran albarkatun kasa da Allah ya azurta kasar dashi.

Ghaddafi ya kasance lokacin rayuwarshi yana ta kira ga kasashen Afrika akan azo ayi takardar kudi ta bai daya wadda zata ragewa dalar Amurka tasiri a yankin nahiyar Africa, amma tun bayan mutuwarshi ba’a kara jin wannan batu ya tasoba.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *