Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa, idan aka zabeshi shugaban kasa a 2023, irin mulkin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi zai yi.
Osinbajo na cikin ‘yan takarar APC sama 20 dake neman jam’iyyar ta basu tikitin tsayawa takarar shugaban kasa.
Wasu dai na zargin Osinbajo da cewa yayi tsaurin ido fitowa takarar shugaban kasar da yayi, a lokacin da me gidansa, Bola Ahmad Tinubu shima yake neman takarar.
Hakanan, Osinbajo ya bayyana cewa shugaba Buhari ya koya mai duk yanda akw mulki.