Mataimakin mai magana da yawun jam’iyyar APC, Yakubu Murtala Ajaka ya yiwa ‘yan siyasar dake neman takarar shugabancin Najeriya a zabe mai zuwa ba’a.
Inda yace Ita dama PDP da Atiku sune manyan kwastoma saboda na biyu suke zuwa a koda yaushe idan akayi zabe, amma kona biyun ma sun kasa wannan karin a jihar Ekiti.
Inda kuma yace shi Peter Obi na jam’iyyar Labour Party haukansa kawai yake yi a kafafen sada zumunta kafin a fara yakin neman zabe.
Yayin da kuma ya cewa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP cewa kar ya yaudari kansa ya dawo APC tun kafin lokaci ya kure masa.