fbpx
Tuesday, September 29
Shadow

Iturralde Gonzalzez: kashi 90 bisa 100 na alkalan wasa masoyan Madrid ne

Tsohon alkalin wasa na kasa Eduardo Iturralde Gonzalez ya bayyana cewa kashi 90 bisa dari na alkalan wasan kasar Spain Masoyan Madrid ne, sai kuma sauran kashi 10 Masoyan Barcelona ne.

Iturralde ya gayawa ‘El Laguero cewa ko Barcelone suna so ko basa so kashi 70 bisa dari  na mutanen kasar Spain masoyan Madrid ne amma banda yan Catalonia.

 

Ya kara da cewa yanzu Barcelona suna da masoya da dawa saboda matasa sunga irin nasarorin da Pep Guardiola ya kawoma kungiyar.

 

Kuma an tambaya Iturralde cewa shin tsakanin Barcelona da Madrid su waye alkalan wasa suke fi nunawa banbanci?, sai Madrid suka fi so domin kamar kashi 90 cikin dari ne.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *