Iyalan mutanen da akayi garkuwa dasu a jirgin kasa na Jihar Kaduna zuwa Abuja sun kai ziyara majalissar wakilai sun roqesu su ceto masu ‘yan uwansu.
Mutane biyu ne suka wakilci iyalan mutanen da akayi garkuwar dasu a ranar 28 ga watan maris na shekarar 2022.
Inda suka ce masu su taimaka a ceto masu ‘yan uwan nasu dake hannun miyagun mutanen da suka yi garkuwa dasu suka kai su cikin jeji.