fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Iyalan wanda aka sace a jirgin kasan dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja sun baiwa gwamnatin tarayya awanni 72 su dauki mataki

Iyalan wadanda aka yi garkuwa dasu a jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja sun nemi gwamnatin tarayya cikin awanni 72 da ta tabbatar an sako musu danginsu.

 

Wakilin ‘yan uwan wanda aka sace din, Dr Abdufatai Jimoh, ya bayyana cewa ida  gwamnati bata yi kokarin sakin ‘yan uwansu ba to su zasu yi dukkan mai yiyuwa wajan ganin sun kubutar da ‘yan uwan nasu.

 

Ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya na da ikon kubutar da dangin nasu.

 

Yace bayan sace dangin nasu, sun gana dasu ta waya amma daga nan sai layin wayar ya daina tafiya.

Karanta wannan  Da duminsa:'Yan Bindiga sun kai hari cocin Bishop Kukah sun sace mutane

 

Yace ‘yan Bindigar sun ce zasu tuntubesu amma basu tuntubesun ba. Yace sun yi tsammanin zuwa yanzu gwamnati zata dauki matakin da ya dace amma taki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.