Iyalan wadanda aka sace a harin jirgin kasa dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja sun roki a sako danginsu ba tare da wani sharadi ba.
A yayin mummunan harin da ya faru an kashe wasu mutane inda wasu kuma aka yi garkuwa dasu.
Dan hakane iyalan wanda abin ya shafa suka roki shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taimaka musu a sako musu danginsu.