fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Jack Grealish: Dan wasan Aston villa ya bayar da hakuri gami da karya dokar gwamnati da yayi ta coronavirus

Dan wasan mai shekaru 24 ya bayyana cewa ya bar gidan shi ne don yaje wurin abokin shi a karshen makon duk da cewa an umurce shi daya zauna a gida don a rage yaduwar cutar coronavirus.

Grealish ya sake wani sabon bidoyo a shafin shi na Instagram ayayin da yake cewa yana matukar jin kunya saboda abin da ya aikata a karshen wannan makon. Kuma yace abokin shi ya neme shi sai yasa ya fita.
Ya Kara a cewa yana mai ba mutane shawara cewa kar wani ya aikata irin abun da yayi saboda shima yanzu zai cigaba da bin dokokin gwamnati kuma yaci gaba da killace kanshi a gida. Kuma yace yana fatan kowa da kowa zai yi mai yafara gami da abin daya aikata.
Kaftin din ya tabbatar da cewa abin daya aikata laifi ne kuma yasa kungiyar Aston villa sunji kunya sosai a idon jama’a kuma sun ce za’a yi mai hukunci dai-dai da abin daya aikata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.