Jimullar masu laifuka 160 ne shugaba Buhari yawa Afuwa daga gidajen yarin kasarnan wanda suka hada hadda tsaffin gwamnonin Filato da Taraba, watau Joshua Dariye da kuma Jolly Nyame.
Hakan ya jawo cece-kuce sosai inda da yawa suka yi Allah wadai da yafewa musamman tsaffin gwamnonin.
Saidai gwamnatin tarayya ta kare wannan mataki nata inda tace an daukane dan rashin lafiyar dake damun su.
Akwai kuma masu safarar kwaya da ‘yan damfara da wanda suka saci dukiyar gwamnati da sauransu da aka wa Afuwa.
Ga jadawalin sunayensu;
