fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Jadon Sancho: Manchester United baza su biya sama da euros miliyan 50 ba wurin siyan dan wasan Ingilan

Kungiyar Borussia Dortmund sun bukaci euros miliyan 100 ga duk kungiyar da zata siya Jadon Sancho yayin da dan wasan yake da sauran shekaru biyu a kwantirakin shi. Jadon Sancho yayi kokari sosai a wannan kakar yayin daya ci kwallaye guda
17 kuma ya taimaka wurin cin kwallaye guda 16.

Dan wasan mai shekaru 20 yanada ra,ayin komawa premier lig amma United da Dortmund har yanzu basu sasanta ba yayin da suka bukaci su biyu euros miliyan 100 bayan su sun siyan dan wasan a farashin euros miliyan 8 daga kungiyar City a shekara ta 2017.

United sune kungiyar da keda alamun amincewa da bukatar Dortmumd amma wasu manyan kungiyar a bayan fage sun fadi cewa kudin da Dortmund suka sama dan wasan nasu bai dace da yanayin da ake ciki ba na annobar korona, kuma idan har suna so su siye shi to sai sun rage mai farashi, ana sa ran United zasu yi tsokaci gami da lamarin bada dadewa ba.

Karanta wannan  Kungiyar PSG ta kori kocinta Maurizio Pochettino

Dortmund sun gayama kasuwar jari ta kasar jamus cewa buga wasan da ake yi ba tare da yan kallo ba zai sa su rasa euros miliyan 41. Dan wasan Birmingham City Juge Bellingham zai taka muhimmiyar rawa a wannan lamarin yayin da ake sa ran dan wasan zai zabi kungiyar da zai koma tsakanin Dortmund ko United.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.