fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Jadon Sancho na cin kwallaye kamar Cristiano Ronaldo lokacin da yake matashi

Jadon Sancho ya janyo ra’ayin kunyoyin zakarun premier lig kuma yanzu dan wasan zai bugawa kungiyar shi ta Dortmund wasa tsakanin su da Schalke a ranar sati, yayin da hukumar Bundlesliga suka shirya cigaba da buga wasannin a karshen wannan makon.

Jadon sancho ya cika shekaru 20 a watan maris kuma ya zamo daya daga cikin zakarun matasan yan wasan tun da ya koma Dortmund daga kungiyar Manchester City a shekara ta 2017.
Dortmund sun sama dan wasa farashin euros miliyan 100 kuma suna fatan ya cigaba da wasa tare da su.
Amma wani makusancin dan wasan yace Sancho zai iya barin kungiyar yayin da United, Liverpool da Chelsea suke cikin kungiyoyin dake harin siyan dan wasan. Sancho yana kokari sosai kafin a dakatar da wasanni yayin da yayi nasarar jefa guda 14 kuma ya taimaka wurin cin kwallaye guda 15 a wasanni guda 23.
Gabadaya kwallayen da Sancho yaci da kuma wanda ya taimaka sun kama 29 kuma hakan yasa mutane kacal suka wuce shi a nahiyar turai kuma dayan su Messi ne. Kwallayen Sancho har sun wuce na Hazard da Sterling kuma yana cin kwallaye da yawa kamar Cristiano Ronaldo lokacin yana matashi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.