fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Jadon Sancho ya kafa tarihi a kwallon kafa ta kasar Ingila da gasar Bundesliga yayin daya ci kwallaye uku (Hat trick)

A jiya 31 ga watan mayu Jadon Sancho yayi nasarar kafa tarihi a kwallon kafa ta kasar Ingila da kuma gasar Bundesliga yayin daya ci kwallaye har uku a wasan su da Paderburn wanda suka tashi 6-1.

Sancho ya bayyana wata riga wadda aka rubuta ” a yiwa George Floyd adalci ” yayin daya jefa kwallon shi ta farko bayan Thorgan Hazard ya jefa tashi kwallon. Jadon ya jefa kwallon shi ta biyu a minti na 74 yayin da kuma ya jefa kwallon shi ta uku gab da za’a tashi wasan.
Yanzu kwallayen Sancho sun kai 15 a wannan kakar wasan, yayin daya zamo dan wasan ingila na farko daya cin kwallaye 15 kuma ya taimaka wurin cin kwallaye guda 15 a kakar wasa guda cikin manyan gasar nahiyar turai guda biyar, tun lokacin da Matt Le Tissier yayi hakan a kungiyar Southampton ta Premier lig shekara ta 1994-95.
Nasarar da Dortmund suka yi tasa yanzu sun samu maki 60 yayin da suka kerewa Borussia Monchengladbach da Bayern Leverkusen da maki hudu, Amma duk da haka zakarun gasar sun fi su da maki bakwai wato Bayern Munich.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  'Yan wasan Manchester sun bukaci a sayar da Ronaldo kuma har yanzu baya jituwa da sabon kocin kungiyar

Leave a Reply

Your email address will not be published.