fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Jahilan ‘yan Arewane ke mulkar Najeriya kuma sunata turo matasansu zuwa kudu dan kaddamar da jahadi>>Kungiyar kare muradun Yarbawa

Jigo a kungiyar kare muradun yarbawa ta Afenifere, Femi Okurounmu ya bayyana cewa yawanci jahilan ‘yan Arewane da kodai basu da ilimi ko kumama kwata-kwata basu yi karatu ba ke mulkar Najeriya.

 

Yayi wannan Maganane akan cikar Najeriya shekaru 21 akan mulki inda yace matasansu na kudy sai yawo a kan titi amma babu aikin yi. Amma matasan Arewa duk sai aiki ake basu duk da cewa ilimin su bai kai na ‘yan kudun ba.

Ya bayyana cewa kaso 50 na matasan Najeriya da suka gama makaranta basu da aikin yi kuma mafi yawancinsu ‘yan kudu ne dan sune suka fi damuwa da karatu. Yace uba zai yi iya bakin kokarinsa wajan ganin ya baiwa dansa ilimo amma haka zai gama ya koma yana yawo a titi babu mafita.

 

Yace idan Dan kudu da dan Arewa suka je makaranta zaka ga dan kudu yayi kokari ya kammala marantar da sakamako me kyau amma dan Arewar da ya sha da kyar ya gama da samakon ba yabo ba fallasa shine bayan kammala makarantar zai samu aiki kuma ya zama ogan dan kudun.

Karanta wannan  Ko ana ha maza ha mata Peter Obi ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya ba a shekarar 2023, cewar tsohon shugaban hukumar Delta

 

Yace shiyasa matasan Kudu hanyarsu daya ta samun sa’ida itace su fita zuwa kasar waje dan neman abin yi.

 

Ya kara da cewa, koda fa ranar 29 da aka mayar da ita ranar Dimokradiyya an yi hakanne dan wulakantar da kabilar yarbawa dan a irin wannan rana ce a zamanin mulkin tafawa Balewa aka saka dokar ta baci a yankin yarbawan aka kuma yiwa Awolowo daurin talala sannan aka kama da yawa daga cikin masu fafutukar yankin.

 

Yace kwanannan a ci gaba da kokarin mayar da ‘yan kudu bayi, Hausawa sai aiko da matasansu suke zuwa kudi wasu da makamai a yawan lokuta kuma idan sun je kudin sai a nemi inda suka yi a rasa.

 

Yace hakan yunkuri ne da wasu da yawa ke tunanin na kaddamar da Jihadi ne dan mamaye yankin Kudu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.