Hukumar ‘yan sandan babban birnin tafayya Abuja sun yi nasarar kwato motoci a hannun barayi ranar juma’a.
Mai magana da yawun hukumar, Josephine Adeh ce ta bayyanawa manema wannan labarin.
Inda tace da misalin karfe biyu na dare ne aka sanar dasu cewa barayi 15 sun afka wani gida a yankin Lugbe.
Kuma jami’a sun hanzarta zuwa gidan sunyi musayar wuta da barayin har sukayi nasarar kwace kayyakin da suka sata hadda motoci.