fbpx
Sunday, May 22
Shadow

Jama’a na cikin halin Matsi>>Sarkin Musulmi

Me Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar na III ya bayyaba cewa jama’a a Najeriya na cikin wani hali na matsi inda ya jawo hankalin shuwagabanni dasu mayar da hankali wajan cire kasar daga halin data tsinci kanya.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Sarkin ya bayyana hakane a jiya, Asabar wajan bikin cikar sarkin Zazzau,Alhaji Shehu Idris shekaru 45 akan karagar mulki. Sarkin Musulmi yawa Sarkin Zazzau jinjina kan jagorancin da yayi a Zazzau da Najeriya baki daya.

Ya kuma yiwa sarkin fatan kyakykyawan karshe. Sarkin ya kuma godewa malaman Addini kan yanda suje karantar da jama’a komawa ga Allah a kowane hali mutum ya tsinci kansa.

Sarkin yayi kira ga shuwagabanni da su tausayawa Talakawa inda yace kowa yasan cewa ana cikin halin matsi. Ya kara da cewa babu abinda ya gagari Allah kuma zasu ci gaba da yiwa shuwagabanni addu’a.

Karanta wannan  Dakarun Sojojin Saman Nijeriya Sun Yi Babbar Nasara Akan ‘Yan Boko Haram

Sarkin ya jawo hankalin mutanen Kaduna da su rika saka shugaba Buhari a addu’a da kuma gwamnan Kadunan inda yace kokarinsu kadai bazai wadatarba dan haka suna bukatar addu’a.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.