fbpx
Thursday, March 4
Shadow

Jama’ar gari sun yi bata kashi da ‘yan Bindiga da suka kai musu hari a Zamfara inda aka kashe wasu

Yan Bindiga sun kai hari a kauyukan Dutsin Gari da Rayau dake karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

 

Wani shaida, Malam Ibro Maman yace yan bindigar sun shiga garin Dutsin Gari da niyyyar sace mutane amma sai ‘yan garin suka musu kawanya. Yace an yi bata kasho tsakanin mutanen garin da ‘yan Bindigar wanda ya dauki tsawon lokaci.

 

Yace da ‘yan Bindigar suka ga ba zasu yi nasarar satar mutanen ba sai suka budewa muta wuta suka kashe 6 da jikkata wasu inda suka nufi kauyen Rayau.

 

Yace a Rayau ma mutane sun ki yadda inda suka yi ta bata kashi da ‘yan Bindigar wanda anan ma ‘yan Bindigar suka kashe mutane amma basu yi nasarar satar kowa ba, haka suka tafi.

Saidai da safiyar yau ma ‘yan Bindigar sun sake komawa kauyukan amma mutanen yawanci sun tsere,  dalilin haka yasa suka bangawa gidaje kusan 40 wuta inda suka sace kayan amfani da dama.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *